Daga Isyaku Garba | Birnin kebbi | 17/6/2018
Alamomin tabin hankali ko hauka basu bayyana farat daya, lamari ne da ke bayyana cikin tsawon lokaci bisa yadda cutar ta shafi mai fama da ita. Amma ga wasu fitattun alamu da ke iya nuni da cewa mai yiwuwa wanda ke jin irin wadannan alamomi ba mamaki yana fama da yiwuwar tabin hankali.
Da zarar ka ji alamar daya daga cikin wadannan alamu sai ka yi sauri ka garzaya zuwa wajen Likita domin a duba ka:
1 Idan kana yaan samun damuwa wajen yin tunani ko mayar da hankali a kan wani lamari.
2 Idan ka ji cewa ka fara zargin makwabta da jama'a da ke tare ko kewaye da kai
3 Idan kana jin sauti ko wata amsa kuwa da ba wanda ke ji sai kai kadai
4 Idan ka kaurace wa masoyanka amma ka fi son ka zauna kai kadai alhali ba haka kake ba a da can.
5 Idan wata sabuwar akida ta shigo tunaninka kuma ba wanda zai gamsar da kai cewa ba gaskiya bane.
6 Idan ka fara daina yin wanka kuma ka daina kula da lafiya ko tsabtar jikin ka
7 Idan ka fara jin wani nau'in matsanancin bacin rai ko bakin ciki a ka da yaushe
8 Idan ka kula cewa ka fara jin haushin masoyanka haka kawai ba tare da sun yi maka laifi ba ko jin haushin mutane ko wani mutum ko mata
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001.
Shiga cikakken shafinmu.
www.isyaku.com
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI