Abin da ya kamata ka sani game da mai shari'a da ke tura Gwamnoni Kurkuku

Cikin 'yan makonnin da suka gabata ne wannan mai shari'a ta yi wani abin da ba kasafai ake gani alkalai maza ko mata ke yi ba a Najeriya, inda ta yanke wa tsoffin gwamnonin kasar biyu hukuncin zaman gidan kaso.

Wace ce wannan jarumar mai shari'a wadda ba ta ji tsoron daure manyan mutanen da ta samu da laifin halatta kudin haram ba?

Sunanta Adebukola Banjoko. Mai shari'a ce a babbar kotun Abuja da ke Gudu.

Ita ce ta yanke hukuncin daure tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame, da kuma tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye.

Ta yanke musu hukuncin zaman gidan yari na shekara sha hudu-hudu ne bayan da ta same su da laifukan cin-amana da kuma halatta kudin haram.

Wace ce wannan 'gwarzuwa'?

  • An haife ta a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya
  • Ta yi karatun digirinta a fannin shari'a a Jami'ar Landan
  • Ta je makarantar koyon shari'a ta Najeriya tsakanin 1985 zuwa 1986
  • Ta dan fara aikin shari'a kafin daga bisani ta zama majistare da jihar Oyo daga 1997 zuwa 2003.
  • A shekarar 2003 ne ta zama mai shari'a a Babbar Kotun birnin tarayyar Najeriya.

"Ta ki jinin a zarge ta da rashin adalci"

An taba kai shari'ar wani tsohon dan majalisar wakilan Najeriya, Farouq Lawan gabanta.
Ana dai zargin Farouq Lawan ne da lafin karbar na goro daga hannun attajirin nan na Najeriya, Femi Otedola, domin cire sunan kamfaninsa, Zenon Oil, daga sunayen wadanda suka yi ba daidai ba da kudin tallafin mai.

Sai dai mai kare Lawan din, Mike Ozekhome, ya nemi Banjoko da ta kaurace wa shari'ar domin yiwuwar bin son rai a shari'ar saboda alakarta da Otedola.

Sai dai kuma daga baya Ozekhome ya janye kiran da ya yi.

Duk da haka mai shari'a Banjoko ta janye daga shari'ar tana mai cewa tun da ta fara aiki a matsayinta ta mai shari'a shekara 17 da suka wuce, ba a taba nuna shakku kan adalcinta ba.
Ta bayyana kiran a matsayin wani abin kunya

Aiki dalla-dalla

Mai shari'ar dai ta kasance tana bin muhawara dalla-dalla kafin ta yanke hukunci, kamar yadda hukuncin da ta yanke wa tsaffin gwamnonin biyu ya nuna.

Ta shafe kimanin sa'o'i shida-shida a lokacin da take gabatar da shari'arta a kan gwamnonin biyu tun daga safiya zuwa yamma.

A lokacin shari'ar Mista Dariye ma sai da ta nemi izinin lauyoyi domin ta tsallake wasu bangarori na muhawara da aka yi a gabanta, da kuma yadda ta yi ta yanke hukunci a kansu.

Ta ce ta yi hakan ne domin ka da a kai dare a kotun, tana mai shaida wa lauyoyin cewa za su iya karanta wadannan bangarorin a cikin takardar shari'ar da aka riga aka ba su.

Bayan ta samu Joshua Dariye da laifi, daya daga cikin lauyoyin tsohon gwamnan ya ce ba a yin nasara idan aka daukaka kara game da shari'ar mai shari'a Banjoko, saboda yadda take bin diddigi a aikinta.

Sai dai kuma mai shari'ar ta nemi ta nuna ba hakan ba ne.

Amma wani dan jarida wanda yake rahoto kan bangaren shari'a ya shaida wa wakilin BBC cewar yana da wuya a yi nasara idan aka daukaka kara game da hukuncin mai shari'ar, saboda yadda take aikinta dalla-dalla

'Dariye tamkar abokina ne'

A lokacin da take karanta shari'arta kan lamarin Dariye, Banjoko ta dage zaman kotun sau biyu domin bai wa tsohon gwamnan jihar Filato din damar zuwa ban-daki.

Kuma ta ce a iya lokacin da aka dauka ana shari'ar ita ta dauki Dariye din tamkar abokinta ne.
Ta yi wannan bayanin ne a lokacin da take yanke masa hukunci.

Ta ce ta daure shi ne saboda hakan ya zama izina ga mutane kan aibun cin hanci da rashawa.

"Ba ta nuna fushi"

Bayan ta sami Dariye da laifi, mai shari'ar ta bai wa lauyoyin hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati (EFCC) da kuma na tsahon gwamnan jihar Filato din damar yin bayanai game da irin hukuncin da ya kamata ta yanke wa mai laifin.

Lauyan EFCC (Rotimi Jacobs) ya nemi mai shari'ar ta yi wa Dariye daurin da ya fi muni domin mutane su guje wa irin laifin da ya aikata.

A lokacin da yake wannan maganar sai Dariye ya yi ta daga hannu yana neman ya yi magana.
Shi kuwa mai kare Mista Dariye ya nema masa afuwa, yana mai cewa ba za su daukaka kara ba domin idan an daukaka kara kan shari'arta ba a yin nasara.

Daga baya ta bai wa dariye damar magana inda tsohon gwamnan ya ce ya kamata Lauya Jacobs ya nuna tausayi a matsayinsa na mai bin addinin Kirista.

Mai shari'a Banjoko ta ce ita ba ta matsala da tsohon gwamnan kuma ma wasu ma'aikatan kotu suna ganin ta fiye yi wa mai laifin sassauci.

Amma kuma da ta ke yanke masa hukunci, ba ta nuna wani bacin rai ba, duk da cewa ta ce bai kyautu ba a ce tsohon gwamnan ya fi jiharsa kudi a lokacin da yake mulki ba tare da cewa ya samu kudin ta sahihiyar hanya ba.

Tana murmushi ta yanke masa hukuncin daurin shekara 14 bisa laifukan da ya yi
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

BBC
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN