Zullumi a Birnin kebbi kan shari'ar Jokolo a Kotun koli Abuja - ISYAKU.COM

Babban Kotun koli na Najeriya a yau, za ta saurari daukaka kara da Sarkin Gwandu na 20 Alh. Muhammad Bashar ya shigar a kan hukunci da Kotun daukaka kara ta bayar cewa a mayar da Sarkin Gwandu na 19 da aka tumbuke a karagar muki Alh. Al-Mustapha Jokolo.

A wani hukunci da wata Kotun daukaka kara da ke Sokoto ta zartar ranar 14/4.2016, cewa a mayar da Sarki Gwandu na 19 Alh. Jokolo a karagar mulki .Kotun ta kuma bayar da umarni cewa a biya basaraken kudadensa na albashi na tsawon shekara 10.Kotun ta aminta ne da wani hukunci da wata babban Kotun tarayya ta zartar a kan karar a Birnin kebbi.

Sarkin Gwandu na 20 Alh. Muhammada Bashar, ya garzaya Kotun koli ne yana kalubalantar hukuncin Kotun daukaka kara, kuma yana bukatar Kotun koli ta jingine umurnin Kotun daukaka kara, kuma ya ce an nada shi a bisa ka'ida bayan tumbuke Jakolo daga Karagar mulki da Gwamnatin Alh. Adamu Aliero ta yi a 2005.


Yanzu haka wannan lamari ya haifar da rudani da zaman zullumi daga bangarori guda biyu, bangaren Jokolo wadanda yawanci 'yan tsohon garin Birnin kebbi ne, da kuma bangaren Sarki Illiyasu wanda tsohon Janar na soji ne kamar yadda Jokolo ma tsohon Manjo ne na soja, kuma dukkansu 'yan gidan Sarautar ta Masarautar Gwandu.

Sakamakon haka, yanzu kowa ya kasa kunne domin sauraron yadda hukuncin shari'ar da ta dauki shakara 13 ana yi zai zo karshe, ko waye Kotun koli za ta ba gaskiya? ganin cewa hukuncinta shi ne daga ke sai Allah ya isa.

Daga Isyaku Garba

Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN