Rahotanni daga babban Kotun koli na tarayya Abuja sun ce an dage
sauraron shari'a tsakanin Sarkin Gwandu na 20 Alh. Illiyasu Bahar da
tsohon Sarkin Gwandu Alh. Al-Mustapha Jokolo har zuwa ranar 19 ga watan
Fabrairu 2019.
Tuni dai wannan shari'ar ya yi fama da dage-dage kuma yanzu haka shekara 13 kenan ana wannan shari'ar.
Koma
yaya za ta kaya a tsakanin Sarakunan guda biyu 'yan gida daya sakamakon
hukuncin Kotun da daga ita sai Allah ya isa, lokaci ne kadai zai
tabbatar da haka.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001.
Shiga cikakken shafinmu.
www.isyaku.com
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI