• Labaran yau


  Karanta sharudda 12 da Amurka ta gindaya wa Iran kan batun nukiliya

  Amurka ta ce ta gindaya wa kasar Iran sharruda 12 wadanda idan ba ta cika su ba, za ta kwashi kashinta a hannu:

  Sharadi na farko: Ta dakatar da sarrafa makashin nukiliya na Plutonuim da kuma rufe dukkanin cibiyon kera makaman kare dangi.

  Sharadi na biyu:  Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA damar shiga illahirin cibiyoyinta na sarrafa makamashin nukiliya da ke fadin kasar.

  Sharadi na uku: Dakatar da kera ko kuma gwaje-gwajen mamakai masu linzami

  Sharadi na hudu: Sakin dukannin Amurkawa da Turawan da ta garkame

  Sharadi na biyar: Dakatar da tallafa wa kungiyoyin ta'adda,wadanda suka hada da Hizbullah,Hamas da Islamic Jihad.

  Sharadi na shida: Martaba gwamnatin Iraki,tallafa wa wajen karbe makamai daga hannayen mayaka 'yan shi'a don ba su damar damawa da su a cigaban kasar.

  Sharadi na bakwai: Dakatar da bai wa tallafi ga mayakan Houthi da kuma neman hanyoyin warware rikicin Yaman cikin ruwan sanyi.

  Sharadi na takwas: Janye dukkanin sojojin daga kasar Sham

  Sharadi na tara: Dakatar da tallafa wa Taliban a Afganistan da kuma karbar bakwancin 'yan kungiyar Al Qaida.

  Sharadi na goma: Dakatar da tallafa wa mayakan Qudus da magoyan bayansu a duniya.

  Sharadi na sha daya: Kawo karshen barazanar da ta ke yi wa kasashen makwabtanta,Amurka da kawayenta da kuma lashe aman da ta yi game da yunkurinta na kauda Isra'ila da doron duniya da kuma dakatar kai wa Saudiyya hare-hare.

  Sharadi na sha biyu: Bai wa hukumar kula da makamashin nukiliya na kasa da kasa (IAEA) cikakken rahoto game da shirinta na nukiliya na da,haka zalika ta yi watsi da aiyukan kera makaman nukiliya har abada.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

  #TRT 
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Karanta sharudda 12 da Amurka ta gindaya wa Iran kan batun nukiliya Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama