Waye kwatankwacin Faruku Enabo a Masarautun Argungu,Yauri da Zuru ?

Yayin da zaben 2019 ke gabatowa wanda za a yi kasa da wata tara, shugabannin siyasa da na al'umma sai kara zage damtse suke yi domin ganin sun sami jama'a wadanda suke ganin za su kada masu kuri'a a 2019.

Haka lamarin yake ko'ina a fadin Najeriya, da yawa daga cikin wadannan 'yan siyasa sukan dasa wasu mutane da za su biya bukatar jama'a a karkarar da suke zaune.

Idan muka waiwaya baya a siyasar jihar Kebbi, lokacin Gwamnatin Alh. Adamu Aliero, kusan Aliero ya dauki salon siyasar dasa mutane kuma a samar masu da dama da za su iya share ma talaka hawaye na lalurar N100.000 ko fiye ba tare da an zo Birnin kebi ba.

Hakan ya yi tasiri kwarai a harkar siyasar waccan lokaci wanda ya haifar da farin jini da ke bin wannan dan siyasar har ranar yau.

To amma a wannan Gwamnati ko akwai tanadin haka a kananan hukumomi duk da yake kowace Gwamnati da irin nata salo da tsarin shugabanci ?.

Mai taimaka wa Gwamnan jihar Kebbi Faruku Yaro Enabo, ya shahara wajen bayar da taimako ga talakawa, kungiyoyi, mabukata da sauransu wanda haka ya jawo masa farin jinin gaske ga matasan jihar Kebbi, musamman a garin Birnin kebbi da kewaye.

Saidai sakamakon jin ra'ayin jama'a da muka gudanar a Masarautar Zuru, Yauri da Argungu ya nuna cewa matasan wadannan Masarautu suna bukatar wakilci ingantacce kamar irin na Enabo a Masarautunsu ganin cewa ana zargin Enabo da rashin daukar wayar salula na mutane da baya da lambarsu kuma baya mayar da sakonnin SMS idan an tura masa face sai yana da lambarka.

Amma wata majiya da ke kusa da Enabo ta shaida mana cewa rashin amsa waya ko mayar da sakon SMS na da nasaba da yanayin aikinsa na mai taimaka wa Gwamna watau P.A tare da yin la'akari da irin nauyi da ke dauke da wannan mukami.

Binciken mu har'ila yau ya tabbatar da cewa Gwamna Atiku Bagudu da kanshi yana mayar da sakonnin SMS da aka aika mashi idan ya sami dama wanda hakan ya kara masa kwarjini da mutunci a idanun matasa da talakawan jihar Kebbi.

Al'umar jihar Kebbi da matasa sun sa ido kwarai ganin yadda harkar siyasar jihar Kebbi ke tafiya, tare da zaton samun cika alkawurra da 'yan siyasa da ke kan mulki suka yi masu a lokacin yakin neman zabe da aka yi kafin zaben 2015.

Daga Isyaku Garba

Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN