Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta yi kokari domin ganin ta tabbatar da nassarar akida da ta sa gaba na yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya duk da yake an tsare shi har tsawon shekara uku lokacin da ya yi kokarin ganin ya fuskanci wannan matsalar a zamin mulkinsa na soja.
Shugaba Buhari ya yi wannan jawaji be a likacin da yake bude sabon ginin hedikwatar hukumar EFCC a Abuja ranar Talata.
Ya ce a karon farko lokacin shugabancin sa na soji cin hanci da rashawa ya yi nassara a kansa a lokacin da ya yi kokarin dakatarwa.
Gwamnatin Buhari ta daure da yawa daga cikin 'yan siyasa na jamhuriya ta biyu bisa laifin cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati.Amma daga bisani aka kifar da gwamnatinsa a wani juyin mulki na cikin gida wanda kwamandan sojin kasar na waccan lokacin Janar Ibrahim Babangida ya jagoranta kuma daga bisani ya dare karagar mulki har tsawon shekara takwas.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001.
Shiga cikakken shafinmu.
www.isyaku.com