Kebbi: An hade 4+4 da BBSO waje daya, sun zama APC campaign Organisation

An hade kungiyoyin siyasa guda biyu na 4+4 da BBSO wadanda ke karadin ganin shugaba Buhari da gwamana Bagudu na jihar Kebbi sun sake tsayawa takara tare da lashe zaben 2019 zuwa dunkulalliyar kungiya guda daya.

Wata sanarwa da ta fito daga fadar gwamnatin jihar Kebbi ta hannun babban Sakataren watsa labarai na Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Mu'au Dakingari ya ce tsoho Gwamnan jihar Kebbi Sanata Adamu Aliero ne ya shaida wa manema labarai haka jim kadan bayan wata ganawa da masu ruwa da tsaki a jam'iyar APC suka yi a fadar Gwamnati.

Adamu Aliro ya ce an aminta gabadaya da rushe kungiyoyin 4+4 da BBSO kuma an hade su waje daya sakamakon haka sun zama APC Campaign Organisation.Ya kara da cewa duk ofis-ofis da motoci da bana-bana da aka rubuta 4+4 ko BBSO duka za a mayar da su APC Campaign Organisation.

Wannan ya biyo bayan wani hargitsi ne da kaddamar da ofishin 4+4 ya haddasa inda wasu kalamai na cin zarafi da batanci suka fito daga bakin wasu 'yan siyasa lamari da ya rikide zuwa hare-hare kan ofishin BBSO a fadin garin Birnin kebbi.

Taron ya aminta da nada Alh. Sulaiman Muhammad Argungu a matsayin Darakta janar na sabuwar kungiyar yayin da shugaban karamar hukumar Jega Barr. Shehu Marshal ya zama mataimakinsa.

Daga Isyaku Garba

Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN