Akalla 'yan
kungiyar ta'adda ta PKK 4448 ne sojojin Turkiyya suka aika barzahu a
yankin Afrin kasar Sham,tun a lokacin da suka fara da kaddamar da
farmakan tabbatar tsaro na "Reshen Zaitun" a yankin.
Ma'aikatar
tsaron Turkiyya ce ta yi bayani game da hare-haren "Reshen Zaitun" da
sojojin kasar Turkiyya suka kaddamar a yankin Afrin na Sham tun a ranar
20 ga watan Janairun bana, da zummar ganin 'yan ta'addar PKK/KCK/PYD-YPG
da na DEAÅž da kubuto yankunan 'yan uwa Musulmai daga zalunci da
cuzgunawar haramtattun kungiyoyin.
A
cewar bayanin,tun farkon Hare-haren na "Reshen Zatun" ya zuwa
yau,sojojin Turkiyya 54 suun yi shahada inda wasu 223 kuma suka jikkata.
Ana
ci gaba da lalata bama-baman da aka binne a yankin Afrin,wanda sojojin
Turkiyya da dakarun Free Syrian Army suka kubutar a ranar 18 ga watan
Maris na bana.
A jimillance a lalata bama-bamai 373,wadanda 159 an kera su da hannu.
Sojojin
Turkiyya tare da tallafin Hukumar ba da tallafi da agajin gaggawa ta
dake karkashi ofishin Firaministan Turkiyya (AFAD),Hukumar Red Crescent
ta Turkiyya da kuma wasu kungiyoyin agaji na Majalisar Dinkin, na ci
gaba safa da marwa don ganin rayuwa ta sake dawowa daidai a yankin na
Afrin.
An sanar da cewa za a ci gaba da
kara kaimi wajen kaddamar da hare-haren na "Reshen Zaitun" har sai an ga
bayan illahirin 'yan ta'adda,samar kwanciyar hankali da zaman lafiya
mai dorewa a karkashin inuwar karamci da kuma dokokin kasa da kasa.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
#TRT