Gwamnatin Najeriya ta biya wasu ‘yan kasar 14,
ladan naira miliyan 439, sakamakon yadda suka taimakawa gwamnatin, wajen
karbo kusan naira biliyan 14 daga masu gujewa biyan kudaden haraji.
Yayin
da take karin bayani akan biyan kudaden, ministar kudin Najeriya Mis
Kemi Adeosun ta ce kyautar ta banbanta da wadda aka fi ta karrama masu
fallasa kudaden sata, kasancewar mutanen 14 sun taimakawa gwamnati ne
wajen fallasa masu kaucewa biyan gwamnati haraji.
Ministar ta kara da cewa gwamnatin Najeriya tana kan shirin gurfanar da masu aikata lafin kin biyan haraji a kotu, nan da zuwa karshen watan da muke ciki, a lokacin da wa’adin yiwa masu aikata lafin afuwa zai kare.
Adeosun ta ce tun bayan da gwamnatin Najeriya ta kaddamar da fara amfani da shirin fallasa masu kin biyan haraji da aka yi wa lakabi da VAIDS a shekarar 2017, an bankado jimillar kamfanoni da kuma attajirai sama da 130,000 da suka aikata laifuka kaucewar biyan haraji.
A bangaren masu fallasa kudaden haramun ko na sata kuma, Ministar kudin ta ce zuwa watan Yuni na shekarar 2017 da ta gabata, gwamnatin Najeriya ta samu biyan naira miliyan 375, 875 ga wadanda suka wasu mutane 20 da suka taimaka wajen kwato kudaden sata da yawansu ya kai naira Biliyan 11, da miliyan 635,000,000.

Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
#RFI