Aikata ba daidai ba da karamar yarinya a Badariya, Kotu ta dage zamanta

An ci gaba da sauraron shari'ar wani dan kabilar Igbo da ake zargi da aikata ba daidai ba da wata karamar yarinya a unguwar Badariya makonnin baya a babban Kotum Majistare ta 1 da kegarin Birnin kebbi.

'Yan makonnin baya ne wasu mutane suka tayar ta 'yar hayaniya bayan sun yi zargin cewa wanda ake zargin yana aikata ba daidai ba a unguwar.

Amma wata majiya ta shaida mana cewa tuhumar da mahukunta ke yi masa ba na aikata fyade bane, tuhumaa ce da ke da alaka da zargin yaudarar karamar yarinya da aikata ba daidai ba.

Lauyan wanda ake zargi ya gabatar da hujjoji daga littafan shari'a na dalilai da zai sa Kotu ta yi watsi da karar.

Amma Alkalin Kotun ya dage sauraron shari'ar har zuwa ranar 15 ga watan Mayu 2018 yayin da aka sake tasa keyar wanda ake zargin zuwa Kurkuku

Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN