Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade - ISYAKU.COM

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi sabbin nade-nade a wadansu hukumomin gwamnatin kasar a ranar Alhamis.

Wadanan nan nade-nade na zuwa ne a daidai lokacin da ake tunkarar zaben 2019, wanda shugaban ke takara domin neman wa'adi na biyu.

A baya dai an soki shugaban da jan-kafa wurin yin nade-nade abin da ya sa wasu 'yan jam'iyyarsa ta APC ke cewa "sun tora mota amma ta budesu da kura".

Ya nada Dokta Anasa Ahmad Sabir a matsayin babban daraktan asibitin koyarwa na Jami'ar Usman Dan Fodio da ke Sakkwato.

Sai Dokta Theresa Obumneme Okoli wadda ya nada shi sabon shugaban Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Horas da Malamai da ke garin Umunze a jihar Anambra.

Akwai kuma Dokta Emmanuel Ikenyiri wanda ya nada shugaban Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Horas da Malamai da ke garin Omoku a jihar Rivers.

Har ila yau, Shugaba Buhari ya nada Dokta Pius Olakunle Osunyikanmi a matsayin daraktan wata hukumar ba da agaji wanda ake kira Technical Aid Corps.

A karshe shugaban ya bukaci mutanen da su yi aiki tukuru kuma su kasance masu mutunta dokokin aiki.

Wasu na ganin wadannan nade-naden da shugaban ke yi a 'yan kwanakin nan ba za su rasa nasaba da kokarin gyara kura-kuran da ya yi ba kafin babban zaben na badi.

  • Shekararsa 76
  • An zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 28 ga Maris 2015
  • Ya bayyana aniyarsa ta neman wa'adi na biyu a zaben 2019
  • Ya yi shugaban mulkin sojan Najeriya daga 1984 zuwa 1985
  • An hambare shi a juyin mulki
  • Ya samu shaidar rashin kare hakkin dan adam
  • An yi amanna ba shi da cin hanci da rashawa
  • Mai ladabtarwa ne - a kan sa ma'aikatan gwamnati tsallen kwado idan suka yi lattin zuwa aiki
  • Musulmi ne daga arewacin Najeriya
  • Ya tsallake rijiya da baya a wani hari da Boko Haram ta kai masa

Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

#BBC
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN