Manchester United ce 'kungiyar da ta fi daraja a duniya'

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta sake zama kungiyar da ta fi ko wace daraja a Turai yayin da darajarta ta kai fam biliyan 2,9, in ji kamfanin kasuwanci na KPMG.

Kungiyar ta Ingila ce take kan gaban kungiyoyi ciki har da Real Madrid da Barcelona a nazarin da KPMG ta yi kan darajar manyan kulob-kulob.

Nazarin, wanda aka yi akan kakar 2015-16 da kuma kakar 2016-17, ya yi dubi kan iya samun riba da mallakar hakkin watsa wasanni da farin-jini da nasarar da za ta iya samu nan gaba da kuma darajar filin wasa.

Kungiyar Liverpool da ta kai ga wasan karshe a gasar zakarun Turai tana mataki na shida a cikin jerin sunayen da kamfani ya fitar na kungiyoyi masu daraja.

Daga cikin jerin kungiyoyi 10 na farko da suka fi daraja a Turai cikin 32 da aka yi nazari akansu, akwai kungiyoyin gasar Firimiya shida a sahun farko.

Andrea Sartori, wanda shi ne shugaban sashen wasannin duniya na KPMG kuma wanda ya rubuta rahoton, ya ce darajar harkar kwallon kafa ta karu cikin shekarar da ta gabata.

Ya ce: "jimillar karuwar daraja yana samuwa ne ta dalilai daban-daban, daya daga cikinsu shi ne karuwar kudaden shiga na manyan kulob 32 din, wanda ya kai kashi takwas cikin 100."

"Cinikin musayar 'yan wasa mai jan hankali da kuma karuwar kudin ma'aikata bai hana wadannan kulob-kulob din samun riba ba, yayin da ribar kafin haraji ta karu sau 17 idan aka kwatanta da bara."

Kungiyoyi 10 da suka fi daraja a Turai
  • Manchester United - €3.255bn
  • Real Madrid - €2.92bn
  • Barcelona - €2.78bn
  • Bayern Munich - €2.55bn
  • Manchester City - €2.16bn
  • Arsenal - €2.10bn
  • Chelsea - €1.76bn
  • Liverpool - €1.58bn
  • Juventus - €1.30bn
  • Tottenham - €1.29bn
Bayanai: KPMG


Mista Sartori ya kara da cewa: "Daya daga cikin dalilan da suka kawo wannan karin shi ne tasirin kungiyoyin Ingila da kuma karin tattalin arzikin wasu matsakaitun kungiyoyin da aka yi nazari akansu, wanda ke nuna biyayya ga dokar hukumar Uefa kan adalci kan kudi."

Duk da cewa kungiyoyin Ingila ne suka fi yawa a cikin 10 na farko, akwai karin wasu kungiyoyin Ingila uku- West Ham United da Leicester City da kuma Everton - cikin kungiyoyi 20 da suka fi daraja.

Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

#BBC
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN