Tsohon
Shugaban Kasar Amurka Barack Obama da matarsa Michelle Obama sun sanya
hannu da kamfanin talabijin din yanar gizo Netflix don fara shirya
fina-finai.
Sanarwar
da kamfanin netflix ya fitar ta ce, Obama da Michelle sun sanya hannu
kan yarjejeniyar shirya fina-finai da kamfanin kuma fina-finan sun hada
da kanan dadogaye, na tarihi da ma na labarun gaskiya.
Sanarwar ta ce, fina--finan za su isa ga masu amfani da Netflix su miliyan 125 a kasashen duniya 190.
A
sanarwar da Shugaban Kasar Amurka na 44 Barack Obama ya fitar ya ce,
suna fata shi da matarsa Michelle su fba wa duniya labarai da hkayoyi
masu dadi duba da yadda yabhadu da mutane nau'i daban-daban a raywarsa.
Ita ma Michelle ta ce, a shirye suke da mijinta wajen bayar da kayattun hikayoyi.
Daya
daga cikin manyan jagororin Netflix Ted Sarandos ya ce, Obama da
Michelle na daya daga cikin manyan mutane a duniya da suka yi jagoranci
kuma za su bayarv da gudunmowa sosai a wannan sabuwar sana'a da za su
shiga.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
#TRT