Sakataren
Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ya fitar da jerin sabbin bukatun da
kasarsa ta ke so a amince da su don sake kulla yarjejeniyar Nukiliya da
Iran wadda Donald Trump ya ce sun janye daga cikinta.
A jawabinsa na farko da ya yi, Pompeo ya yi wa Iran barazana da takunkumai mafiya tsauria cikin tarihi.
Ya
ce, sabbin takunkuman da za su saka wa Iran suna da tsauri sosai, kuma
idan Kasar ta ki sauya manufofinta a Gabas ta Tsakiya to Trump zai bullo
mata ta bayan gida.
Pompeo ya
bayyana cewa, Iran ta kasance tana yakar dukkan Kasashen Gabas ta
Tsakiya kuma idan sabbin takunkuman Amurka suka zo to Iran za ta koma
aiyukan neman farfado da tattalin arzikinta.
Ya
ce, za su takurawa Iran ta yi sabon tsari na ko dai ta daina yaki a
Gabas ta tsakiya ko kuma ta ci gaba da asarar kudadenta a kasashen waje.
Ministan
ya ci gabada cewa, idan Iran ta sauya halayyarta to Amurka za ta dawo
da alakar kasuwanci da diplomasiyya da ita tare da ba ta damar habaka
fasaharta ta kere-kere.
Pompeo ya
gargadi kasashen Turai da ke son ci gaba da amfani da yarjejeniyar
Nukiliya da Iran inda ya ce, hakan zai sanya Amurka daukan matakan ba
sani ba sabo.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
#TRT