Sakamakon
kiran da Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip ErdoÄŸan ya yi, Kasashen
Musulmi na duniya sun fara kauracewa kayayyakin da Isra'ila ke samarwa.
A
ranar 20 ga watan Mayu ne Shugaba Erdogan ya ziyarci kasar Bosniya inda
ya gana da Turkawa da ke kasashen waje kuma a lkacin da ya ke kan
hanyar dawo wa ya yi bayani ga 'yan jaridu.
A
jawabin na sa Shugaba ErdoÄŸan ya tabo batun Zalunci da rashin adalcin
da Amurka ta yi na mayar da ofishin jakadancinta da ke Tel Aviv zuwa
Kudus.
Da
aka tambayi ErdoÄŸan ko za a yi aiki da kiran da suka yi na a kaurace wa
Isra'ila da kayayyakinta kamar yadda Kungiyar Hadin Kan Kasashen
Musulmi OIC suka bukata sai ya bayar da amsa da cewa, a matsayinsu na
shugabannin kungiyar OIC sun yi kira ga Kasashensu da su kauracewa
kayayyakin da Isra'ila ke samarwa.
Shugaba
ErdoÄŸan ya ci gaba da cewa, yana fata dukkan kasashe mambobinn OIC za
su yi aiki da wannan kira tare da daina sayen duk wani daga hannun
Isra'ila.
ErdoÄŸan
ya kuma ce, Turkiyya ma za ta dauki mataki hakan inda za su duba duk
wata alaka da suka kulla da Isra'ila a fannon kasuwanci da tattalin
arziki.
Shugaban na Turkiyya ya ce da zarar an kammala zabukan 24 ga watan Yuni za su fara aiki a kan haka.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
#TRT