Mutuwar 'dan acaba ya yi sanadin kone motar 'yansanda - ISYAKU.COM

Kimanin 'yan acaba 3000 da suka harzuka sakamakon mutuwar wani 'dan acaba ranar Talata sun kai hari a wani caji ofis na 'yansanda da niyyar su kone ofishin, amma bayan turjiya daga 'yansanda sai suka nufi Ibeshe a yankin Ipakoda na Ikorodu inda suka banka ma wata motar 'yansanda wuta ranar 30/5/2018 da misalin karfe 10:45 na safe.

Wani bayani da ke da nasSaba da 'yansanda ya ce, lamarin ya faru ne jiya , bayan wani dan acaba ya dauko wani mutum da wata babbar jaka, amma bayan 'yansanda sun tsayar da shi domin bincike, marmakin ya tsaya, sai ya kara wa babur wuta.

Garin tsere wa binciken 'yansanda, sai ya fadi a wani rami, sakamakon haka ya mutu, mai babbar jaka kuma ya yi batan dabo daga wajen sakamakon rudani da ya auku.

Bisa wannan dalili ne washegari 'yan acaba kimanin 3000 suka shiga zanga-zanga da ya kai ga yunkurin kone ofishin 'yansanda tare da kone motar ta 'yansanda.

Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN