Bagudu ya bukaci a inganta yadda ake amfani da Facebook - ISYAKU.COM

Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya ce ba daidai bane ma'abuta amfani da Facebook su dinga amfani da wannan kafar domin mayar da shi wata kafa ta yanke hukunci daga jama'a a kan ayyuka tare da kudirorin gwaamnati yayin da ake cikin yin su kafin a kammala su.

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne ranar Talata a dakin taro na masaukin shugaban kasa a Birnin kebbi yayin da ya halarci wani taro da wata kungiyar matasa ta shirya kan murnar cika shekara 19 na komawa mulkin Dimokradiyya a jihar Kebbi.

Gwamnan ya bayyana cewa "wasu mutane sun mayar da Facebook zauren jin ra'ayin jama'a a kan ayyuka tare da manufofin gwamnati da ake yi".

Ya kara da cewa babu yadda za a yi a sami cikakken bayani a kan wadannan ayyuka domin ana cikin yin su ne ba a kammala ba, amma sai masu amfani da Facebook su yanke hukunci .

Bagudu ya bukaci a tsabtace yadda ake amfani da Facebook domin ganin an sami tsari ingantacce na samar da bayanai masu tsabta tare da sada zumunci.

Daga Isyaku Garba

Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN