Tashar
Talabijin ta Al-Akhbariyya da ke Saudiyya ta bayyana cewa, ‘yan tawayen
Houthi na Yaman sun harba makamai masu linzami 2 zuwa garin Najran na
Kasar amma kuma an yi amfani da garkuwa wajen harbo su kasa.
Amma
tashar Al-Misira mallakar mayakan Houthi ta sanar da cewa, an nufi wasu
cibiyoyin kudi da ke garin Najran a harin kuma an yi amfani da makami
mai linzami samfurin Badir wajen kai harin.
Saudiyya ta sanar da cewa, tun daga ranar 26 ga watan Maris ta lalata makamai masu linzami 28 da aka harba mata daga Yaman.
A
ranar 26 ga watan Maris din 2015 ne Saudiiyya ta jagoranci Kasashen
Larabawa wajen kai wa ‘yan tawayen Houthi na Yaman hare-hare ta sama
kıuma tun daga wannan lokacin zuwa yau an harba wa Saudiyya makamai masu
lizami 132.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Daga TRT