Kakakin
Shugaban Kasar Turkiyya Ibrahim Kalın ya bayyana cewa, har nan da
tashin Alkiyama za a ci gaba da tsare Alkur'ani Mai Tsarki.
Turkiyya ta mayar da martani ga wasu 'yan siyasa marubuta su 300.
Mutanen
sun hada da tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy wadanda suka nemi
da a yi wa Alkur'ani Mai tsark, Kwaskwarima saboda yana dauke da bayanan
nuna kyama ga Yahudawa.
Kakakin na Shugaban Turkiyya Ibrahim Kalın ya ce,
"Alkur'ani
Mai Tsarki ba allon kowa da kowa ba ne na rubuta goge ba. Littafinmu ne
Mai tsarki. Kuma har nan da Alkiyama za a ci gaba da tsare Shi. Kyamar
Yahudawa wani tsarine da ya fito daga Turai. Kasashen Yamma da ke son
magance wannan matsala to su tambayi Kasashensu. Wannan na nuna wauta da
jahilci a zamanin yau."
Shi
ma Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya mayar da
martani ga 'yan siyasar na Faransa da cewa, "Wannan kalami nasu alama
ce ta nuna kyama ga Musulunci. Sun wuce gona da iri. Idan aka yi irin
wadannan kalamai me ya ke faru wa a Turai? Sai a lkai hare-hare kan
Masallatan Juma'a.
Ya
ce, a tsawon tarihi Kasashen Yamma sun zalunci Yahudawa. Kun zalunci
Yahudawa, Daular Usmaniyya da Jamhuriyar Turkiyya. Musulmai ne suka
tsare su.
CavusoÄŸlu
ya ci gaba da cewa, babu kyamar Yahudawa a wajen Musulmi. Hakan ya sama
wa imaninmu da Alkur'aninmu Mai Girma. Shin wa za ku ba wa darasi.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Daga TRT
Tags:
LABARI