• Labaran yau


  Isra'ila ta shirya domin fuskantar yiwuwar farmakin ramuwar gayya daga Iran

  Kasar Isra'ila tana shirye shiryen fuskantar yiwuwar harin soji daga kasar Iran kan muradun soji na Isra'ila wanda ake kyautata zaton cewa Iran za ta kaddamar da harin ne daga gabacin kasar Syria.

  Isra'ila ta ce ta bankado wani shiri ne da wasu gwanayen kwamandodi daga cikin kungiyar Hizbullah da suka sami horo daga Iran suke shirin kai hare hare kan Isra'ila domin ramuwar gayya a kan wani harin bamabamai da jiragen saman yaki na Isra'ila suka kai a kan sansanin sojin Iran na T4 da ke Syria wata biyu da suka gabata.

  Hizbullah karkashin kwamandan sojin juyin juya hali na Iran Maj-Gen Qasem Soleimani sun sami horo na musamman da za su iya amfani da makamai masu linzami na zamani domin fuskantar Isra'ila daga gabacin Syria.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Isra'ila ta shirya domin fuskantar yiwuwar farmakin ramuwar gayya daga Iran Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama