Type Here to Get Search Results !

Kungiyar Kasashen Musulmi na taron koli a Istanbul a kan Qudus

Kungiyar Kasashen Musulmi ta OIC ta karba kiran shugaba Recep Tayyip ErdoÄŸan akan gudanar da taron koli akan Qudus a birnin Istanbul, kimanin wakilai daga kasashen Musulmi 40 ne suke halartar taron a yau Juma'a.

A taron da shugaba Recep Tayyip ErdoÄŸan ya kira cikin gaggawa a kan lamurkan dake faruwa a Falasdin ya samu halartar shugabanin kasashe 13, Firaministoci 2, mataimakan shugabanin kasashe 3, mataimakan firaminista 12, ministocin harkokin waje 11 da kuma manyan jami'an harkokin waje na kasashe da dama.

A taron shugabanin kasashen da suka hada da na Iran Hasan Ruhani, Afganistan; Asharif Gani, sarkin Jordan 2. Abdullah, Sudan Omer el-Beshir, Gine Bissau  Jose Mario Waz da kuma shugaban Gine Alpha Gonde, Sarkin Qatar Sheik Temim bin Hamed Al Sani, Sarkin Kuwait Sheik Sabah el-Ahmed el-Jabir es-Sabah, Shugaban Moritanya Muhammed Walid Abdulaziz, shugaban Jamhoriyar Demokradiyyar Cyprus ta Turkiyya Mustafa Akıncı, Pakistan Shahid Hakan Abbasi da Kırgızistan Muhammed Kalıy Abılgaziyev sun samu halarta.

Haka kuma mataimakin firministan Indonesiya Yusuf Kalla, mataimakin shugaban kasar Gambiya  Aja Fatoumatta Tambajang, mataimakin Jamhoriyar Demokradiyar Cyprus ta Turkiyya Kudret Özersay, da kuma ministan harkokin wajen kasar, mataimakin firaministan Somali Mehdi 

Muhammed Julid, Mataimakin firaministan Yaman  Abdulmelik el-Mihlaf suna wakiltar kasashen su.
Bugu da kari a taron kolin Kungiyar Kasashen Musulmin firaministan kasar Falasdin Rami el-Hamdallah da Babban Sakataren Kungiyar Kasashen Musulmi Yusuf bin Ahmed el-Useymin sun halarci taron.

Sojojin Isra'ila dai sun budewa Falasdinawa wuta a ranar litinin data gabata a yayinda suke gudanar da zanga-zangar kalubalantar yunkurin Amurka na mayarda ofishin jakadancinta ta kasar Isra'ila zuwa Qudus lamarin da ya haifar da mutuwar Falsadinawa 62 da kuma raunana kusan dubu uku.

Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

#TRT

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN