• Labaran yau


  Gwamnoni na duba yiwuwar karbe ragamar tallafin man fetur daga NNPC


  Majalisar tattalin arziki NEC da ta kunshi jihohi 36 na Najeriya, ta yi barazanar za ta karbe ragamar tafiyar da tallafin man fetur ganin irin biliyoyin dala da NNPC ke kashewa a shekara.

  Shugaban majalisar Gwamna Abdulazeez Yari na jihar Zamfara ya shaida wa manema labarai jim kadan bayan fitowarsu daga taron na NEC wanda mataimakin shubgaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta ranar Alhamis a Abuja. 


  Ya kara da cewa Gwamnonin za su sake zama a kan lamarin a watan Yuni domin duba yiwuwar ko za su karbi ragamar tallafin man fetur daga NNPC wacce take kashe Naira biliyan 800 a kowane shekara.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Gwamnoni na duba yiwuwar karbe ragamar tallafin man fetur daga NNPC Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama