• Labaran yau


  Yadda Isra'ila ta kashe Palasdinawa 106 a kan iyakar Gaza

  Shugaban kwamitin kula da 'yancin bil'adama na MDD ya ce matakin da Isra'ila ta tauka a kan Falastdinawa a kan bakin iyakan Gaza "abu ne da bai dace ba kuma rashin adalci ne" ya kuma yi kira ga kasashen Duniya su gudanar da bincike na kasa da kasa a kan lamarin.

  Yayin da yake jawabi ga zaman MDD kan 'yancin bil'adama ranar Juma'a, Zeid Ra'ad al-Hussein ya ce babu takamammen shaidar cewa Isra'ila ta yi wani kokari domin ganin an kiyaye yiwuwar samun yawan Palasdinawa wadanda za su jikata ranar Litinin sakamakon harin dakarun ta.

  Ya ce askarawan Isra'ila sun kashe Falasdinawa 106 tare da yara 15 tun 30 ga watan Maris. Fiye da Palasdinawa 12.000 ne Isra'ila ta raunata, akalla mutum 3,500 an raunata su ne sakamakon harbi da albarushin bindiga.

  Wannan ya faru ne bayan Palasdinawa sun shafe makonni suna zanga-zanga a kan iyakar Gaza domin ganin Palastinawa 'yan gudun hijira sun koma gidajensu da ke cikin kasar Isra'ila wanda haka ya yi dai dai da shekara 70 na Nakba lokacin dakarun Isra'ila suka kore fiye da Paladinawa 700,000 daga gidajensu,Haka zalika ya yi daidai da mayar da ofishin jakadancin Amurka daga Tel Aviv zuwa birnin Kudu (Jerusalem) ranar Litinin.

  Isyaku Garba

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda Isra'ila ta kashe Palasdinawa 106 a kan iyakar Gaza Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama