Ofishin
Kamfanin dillancin labarai na Anadolu da ke garin Haseke ya bayyana
cewa, aranar Juma'ar da ta gabata wasu manyan jami'an sojin Saudiyya 3
sun je garin Kobani tare da gana wa da 'yan ta'addar na PKK/PYD-YPG a
sansanin Harap Ishk na sojin Amurka.
An samu labarin cewa, Saudiyya da Hukumominta na taimaka wa kungiyar ne don samar da wata runduna ta Larabawa mai karfi.
Saudiyya
ta yi alkawarin biyan dala 200 kowanne wata ga duk wadanda suka amince
da shiga rundunar inda tuni ta kafa cibiyoyi a Haseke da Kamishli.
A
watan da ya gabata Saudiyya ta aike da kayan taimako a tireloli ga 'yan
ta'addar PKK/PYD-YPG da ke arewacin Iraki. Akwai magunguna da makamai
da ma motocin daukar marasa lafiya, amma gwamnatin Saudiyya ba ta ce
komai game da batun ba.
A
watan Oktoban shekarar da ta gabata ministan Saudiyya mai kula da
harkokin yankjin Gulf ya ziyarci jami'an Amrka da ke yankin Rakka da
'yan ta'addar na PKK/PYD-YPG suka mamaye.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI