• Labaran yau


  Kotu ta umurci 'yansanda su mayar da Dino Melaye babban asibitin tarayya Abuja

  Wata babbr Kotu a birnin Lokoja ta bayar da umarnin wucingadi cewa 'yansanda su mayar da Sanata Dino Melaye babban Asibitin tarayya domin ya ci gaba da jinya. Justice Nasir Ajah ya bayar da wannan umaurni ne bayan Lauyan Melaye Mike Ezekhome (SAN) ya bukaci a bayar da belinsa.

  A ranar Alhamis da ta gabata ne 'yansanda suka gurfanar da Dino Melaye a gaban wata Kotun Majistare a garin Lokoja inda aka tuhume Sanata Melaye da ba 'yan daban siyasa makamai domin su tayar da hankalin jama'a.

  Sakamakon haka Alkalin Kotun ya tasa keyar Sanata Melaye zuwa kurkukun yansanda inda zai kasance a hannun 'yansandan har kwana 39. Daga bisani Alkain Kotun ya ki ya aminta ya bayar da belin Sanata Melaye duk da yake Lauyan Melaye ya gabatar cewa sashe na 97 na dokokin Penal Code ya fayyace cewa za a iya bayar da belin wanda ake tuhum a wannan sashe.

  An dage shari'ar har zuwa ranar 11 ga watan Yuni 2018.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kotu ta umurci 'yansanda su mayar da Dino Melaye babban asibitin tarayya Abuja Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama