'Yansanda a Kebbi sun kama mutum 10 bisa zargin kai hari gidan P.A Enabo

Rundunar yansanda a jihar Kebbi ta kama mutum 10 bisa zargin kai hari tare da aikata barna a gidan mai taimaka wa gwamnan jihar Kebbi P.A Faruku Enabo.

Ranar Talata ne wasu matasa suka kai hari tare da barnata wasu motoci a gidan Enabo, haka zalika matasan sun kai hari a ofis na BBSO da ke garin Gwadangaji da gidan man Texaco a Birnin kebbi inda suka aikata barnar dukiya.

Kakakin hukumar yansanda na jihar Kebbi ASP Suleiman Mustapha ya shaida wa manema labarai cewa lamarin zai iya samo asali ne sakamakon kishi da azazza tsakanin kungiyoyin siyasa guda biyu na 4+4 da BBSO wanda ake zargin cewa wasu matasa daga daya bangaren sun kai farmaki a gidan Enabo.

Amma wata majiya ta shaida mana cewa Gwamna Bagudu ya sha alwashin hukunta wadanda suka kai wannan farmaki ga "dan amana" wanda aka ce ya yi wannan furuci ne yayin da ya je ta'aziyya a unguwar gama gira a garin Birnin kebbi ranar Laraba.

Tuni dai wannan lamari ya haifar da mumunar gibi na rashin tabbas ga alkiblar siyasar APC sakamakon yadda lamarin ya raba lissafin fahimtar 'ya'yan jam'iyar da ke biyayya ga bangarorin da suka rikide zuwa kishiyoyin juna guda biyu na 4+4 da BBSO.

Daga Isyaku Garba

Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN