Shugaban
Koriya ta Arewa na tuhumar Trump da ci gaba da yada labaran karya kan
ainahin dalilan da suka sa su dakatar da kera makaman kare dangi na
nukiliya.
A cewar kafar yada labarai ta Koriya ta Arewa KCNA,Kim ya ce:
"A
baya baya nan, Amurka na ci gaba da yada zuki ta malle da gangan,da
nufin alakanta aniyarmu ta
dakatar da kera makaman nukiliya da
takunkuman da suka kakaba mana.Alhali ba haka batun yake
ba.Idan Amurka
za ta ci gaba da murde gaskiya,kallon mu a matsayin matsorata da kuma yi
mana barazana,to ko shakka babu, ungulu za ta koma gidanta na
tsamiya,don ba zamu taba yarda a raina mana hankali ba"
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
#TRT
Tags:
LABARI