• Labaran yau


  Majalisar Dattawa ta ce safeto janar na 'yansanda makiyin dimokradiyya ne

  Majalisar Dattawa ta Najeriya ta ce babban safeto janar na 'yansandan Najeriya Ibrahim Idris makiyin Dimokradiyya ne kuma bai cancanta ya rike kowane mukami ba a cikin da wajen Najeriya.

  Wannan ya biyo bayan wani zama da Majalisar ta yi ne a yau kuma babban safeto janar na 'yansanda bai amsa gayyatar Majalisar Dattawan ba a karo na uku a jere.

  Ana kyautata zaton zai amsa tambayoyi da suka shafi zancen Dino Melaye da kashe kashe da aka yi a jihar Adamawa da sauran sassan Najeriya.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Majalisar Dattawa ta ce safeto janar na 'yansanda makiyin dimokradiyya ne Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama