Zaben shugaban APC a Kebbi, wakilai sun jajirce sai Maccido - ISYAKU.COM

Zaben shugaban jam'iyar APC a jihar Kebbi ya dauki wani salo da ke da rudarwa ga fahimta sakamakon yadda har zuwa karfe 11:45 babu wata matsaya kwakkwara da zai tabbatar da lokacin da za a gudanar da zaben sabon shugaban jam'iyar ta APC.

Tun da sanyin safiya Asabar 19/5/2018 ne aka girka jami'an tsaro na 'yansanda,DSS,NSCDC har da VGN wadanda aka gani suna sintiri a babban filin wasa na Haliru Abdu inda ake zaton a wajen ne za a gudanar da zaben, sai kuma Filin sukuwa inda aka gan jami'an tsaro, kuma ana zaton cewa a nan ne za a tantance wakilai masu kada kuri'a.

Amma zuwa karfe 2 na rana, an gan taron jama'a a harabar gidan Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi wanda ba kasafai ake ganin irin wannan taro da cinkoson jama'a ba . Wanda hakan ya haifar da zargin cewa ana kokarin a daidaita wasu lamura ne a cikin gida dangane da 'yan takarar kujerar shugaban jam'iyar APC a jihar Kebbi.

Wani bawan Allah mai suna Yakubu Musa Sabon Sara daga karamar hukumar Maiyama ya ce "Ni kaina ina daga cikin wadanda za su yi zabe, kuma tun jiya nike shirye amma sai ga shi da tsakar rana na ji wata magana wanda ban ji dadi ba. Na zo da shiri tsakani da Allah domin in zabi tsohon Chiyaman kuma sabon Chiyaman shi ne wanda ka ji jama'a na cewa sai Barista watau Alh. Maccido.

Kananan hukumomi 21 da ke jihar Kebbi in Allah ya yarda yanzu muna da kananan hukumomi 19 a cikin wannan mazabar, kuma duk wanda ke nan shirye yake ya zo a yi zabe amma sai ga shi har yanzu ba a zo aka yi zabe ba, kuma ni dai tsakani da Allah na ji haushi ba a zo aka gwada Chiyamomin nan muka zo muka zabesu ba.

Alhamdu lillahi Chiyaman dan Birnin kebbi ne, kuma Gwamna dan Birnin kebbi ne, mu talakkawa muka yarda da wannan, kuma idan ka gan wasu mutane can daban, ba talakkawan jihar Kebbi bane. Wasu mutane ne masu wata manufa da ban sani ko Gwamnati ta gano su ba, kuma manufarsu ba na son ci gaban talakawan jihar Kebbi bane.

Mu masu da'a ne ga Gwamnati, amma idan Gwamnati ta ce tana bayan wancan, wallahi ta ci zarafin mu, amma muna yi mata da'a a matsayin ta na Gwamnati".

Daga nan ne gaba daya harabar filin Sansanin Alhazai ya rude da sai "Barista sai Barista !"

Wasu bayanai sun nuna cewa ana zargin cewa akwai masu karfin iko tare da fada aji a cikin jihar Kebbi da ke da wata bukata a kan 'yan takaran shugabancin jam'iyar  APC, wanda bincike ya nuna cewa hakan ya ci babban karo da bukatun dubban jama'ar jihar Kebi musamman wakilai da suka zo Birnin kebbi domin gudanar da wannan zaben.

Daga Isyaku Garba a garin Birnin kebbi

Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN