Type Here to Get Search Results !

Bala Sani kangiwa ne sabon shugaban jam'iyar APC a Kebbi - ISYAKU.COM

Masu ruwa da tsaki a jam'iyar APC a jihar Kebbi sun yi matsaya a kan mika shugabancin jam'iyar APC ga Arc. Bala Sani Kangiwa wanda shi ne kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Kebbi kafin wannan nadin.

Majiyar mu ta shaida mana cewa an aminta a mika shugabancin jam'iyar ga Bala Kangiwa ba tare da hamayya ba.

Amma zahiri, babu wata dama da aka ba wasu wakilai domin su gudanar da zabe, kenan nadin Arc. Bala ya zo wa mutane da dama a bazata sakamakon yadda mamaki ya cika fuskokin dimbin jama'a da suka halara domin yin zabe wanda ba a sanar da su cewa nadi ne za a yi ba zabe ba.

Wani Wakili daga karamar hukumar Maiyama da baya son a ambato sunansa, ya shaida mana cewa "dora masu abin son ra'ayi ne ba zabin 'yar tinke na a baje farin jini bane aka yi masu".

Da yawa daga cikin jama'a da suka zo daga wasu kananan hukumomi sun kwana a garin Birnin kebbi har zuwa karfe 5 na yamma suna filin wasa na Haliru Abdu, kuma ba wani jigo a jam'iyar APC ko hukumar zabe da ya bayyana kansa dangane da yadda lamurra ke tafiya.

Daga Isyaku Garba

Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN