• Labaran yau


  "Cutar Ebola ba za ta sanya mu daina cin naman biri ba"

  An bayyana karuwar mutuwar wasu mutane biyu bayan kamuwa da cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyar Kongo bayan sake buluwar cutar da ta yi sanadiyar rayuka 28 kawu yanzu.

  Hakika, al’umar kasar sunki bin shawarwarin da aka basu domin kare kamuwa daga cutar inda suke ci gaba da samar da naman biri a babban kasuwar Mbandaka.

  A hirar da manema labarai suka yi da wata mata mai suna Carine, ta bayyana musu cewar “Mun ki daina cin naman biri duk da an ta’alaka shi da cutar Ebola, mun kasance masu cin naman biri shekara da shekaru, ba zamu daina ba a yanzu”

  Masana wadanda suka yi bincike a lokaci da cutar ta fara bulla a shekarar 1976 sun bayyan cewar, an kamu da cutar ne daga jemagu da namun daji da mutanen yankin ke ci kamar su birai da makamantarsu.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

  #TRT
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: "Cutar Ebola ba za ta sanya mu daina cin naman biri ba" Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama