Gwandu: Hon.Fraruk ya bayar da kyautar shinkafa da N10m ga 'yan mazabarsa

'Dan Majalisar Dokoki na jihar Kebbi mai wakiltar Gwandu Hon. Faruk Muhammed (Pele) ya raba kyautar buhuhuwan shinkafa da kudi fiye da naira Miliyan 10 ga jama'ar Mazabarsa zaman goron Azumin watan Ramadan ranar Asabar.

Wadanda suka amfana da kyautukan sun hada da mutum 360 wadanda suka fito daga Mazabu (Ward) 10 da ke da esko 36 ko wane ya sami N5000.Shugabannin Mazabu (chairman) na kowane Mazaba sun sami N10.000 kowanensu.

Haka zalika esko na karamar hukumar Gwandu sun sami N10.000 kowanensu.

Fiye da mutum 700 ne suka amfana da wannan kyautar ta Hon. Faruk Muhammed mai wakiltar Gwandu a Majalisar Dikokin na jihar Kebbi.

Shugaban jam'iyar APC a karamar hukumar Gwandu Alh. Mamuda Mode Gwandu , ya sami kyautar mota kirar Peugeot 406 daga hannun Hon. Faruku Muhammed.

Daga Isyaku Garba

Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN