• Labaran yau


  Shugaba Buhari ya jagoranci Tafsir a fadar shugaban kasa

  Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci zaman Tafsir a fadar shugaban kasa na Aso da ke Abuja ranar farko ga watan Ramadan.

  Babban Limami Abdulwaheed Abubakar ne ya bude zaman tafsirin da addu'a, ya kuma gode wa Allah da ya ba shuga Buhari lafiya. Shugaba Buhari ya yi doguwar jinya a kasar waje a bara.

  Ya kuma roki 'yan Najeriya su kasance masu tsoron Allah tare da fatan alkhairi ga junansu.

  Haka zalika ya roki Allah ya sa a yi zabe lafiya a kare lafiya a 2019.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Shugaba Buhari ya jagoranci Tafsir a fadar shugaban kasa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama