Hukumar EFCC a jihar Gombe ta gurfanar da wata mai yi ma kasa hidima NYSC a gaban Justice Abubakar Jauro na babban Kotun tarayya bisa zargin cin amana da yin karya domin a karbi kudi.
Wannan ya biyo bayan wata takardar koke da wani Yusuf Idris ya rubuta wa hukumar bisa lamarin mazauni rukunin gidaje na Tumfure da ke Gombe.
Takardar koken ta ce ranar 21 ga watan Maris 2017 wacce ake zargin tare da wasu mutane da suka tsere ta karbi N63.000.00 daga hannunsa da niyyar cewa za su sama mashi aiki a hukumar Kwastam NCS amma suka kasa tabbatar da haka kuma kudinsa suka makale.
Bayanai sun nuna cewa an saka kudin ne a asusun ajiya na Banki wanda ke dauke da sunan Maduako Ugonma Chinomso a Bankin Union Bank Gombe mai lamba 0053158443.
Bayan an karanto mata zargii da ake yi mata, wacce ake zargin bata amsa laifin ta ba sakamakon haka Justice Jauro ya dage sauraron shari'ar har zuwa ranar 16 ga watan Afrilu domin ci gaba da shari'ar yain da aka tasa keyarta zuwa Kurkuku kafin lokacin zaman Kotu na gaba.
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa
isyakulabari@gmail.com
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001.
Shiga cikakken shafinmu.
www.isyaku.com