Yansanda sun cafke wadansu mutum 12 bisa zargin kasancewa da hannu a mumunar fashi da makami da aka yi a garin Offa na jihar Kwara ranar Alhamis da ya gabata.
Mai magana da yawun hukumar yansanda na Najeriya Jimoh Moshood ya yi bayani a kan lamarin tare da fitar da sunayen wadanda aka kama.
Wadanda aka kama bisa zargin kasancewa da hannu a fashin:
i) Adegoke Shogo 29yrs – An kama shi a Offa
ii) Kayode Opadokun 35yrs –An kama shi a Offa
iii) Kazeem Abdulrasheed 36yrs – An kama shi a Offa
iv) Azeez Abdullahi 27yrs – An kama shi a Offa
v) Alexander Reuben 39yrs – An kama shi ranar 11th Aprilu, 2018 a Lagos
vi) Jimoh Isa 28yrs – An kama shi ranar 11th April, 2018 a Lagos
vii) Azeez Salawudeen 20yrs – An kama shi a Offa tare da wayar salula da SIM na wadanda aka kashe a fashin.
viii) Adewale Popoola 22yrs – An kama shi a Offa tare da wayar salula da SIM na wadanda aka kashe a fashin.
ix) Adetoyese Muftau 23yrs – An kama shi a Ibadan na jihar Oyo
x) Aminu Ibrahim 18yrs – An kama shi a Illorin na jihar Kwara
xi) Richard Buba Terry 23yrs – An kama shi a Illorin na jihar Kwara
xii) Peter Jaba Kuunfa 25yrs – An kama shi a Illorin na jihar Kwara
Tuni dai sashen CIID na hukumar yansanda suka shiga aikin bincike gadan-gadan babu kama hannun yaro ganin irin aikin rashin imani da wadannan yan fashi suka aikata a lokacin farmaki a Bankin Union Bank na garin Offa.
Jimoh ya ce dukannin wadanda aka kama sun tabbatar ma yansanda cewa suna da hannu a wannan aika-aika.
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa
isyakulabari@gmail.com
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001.
Shiga cikakken shafinmu.
www.isyaku.com