Type Here to Get Search Results !

Za a mayar da gidan madugun yan tawayen Biafra Ojukwu wajen yawon bude ido

Gwamnatin jihar Anambra ta sanar da cewa za ta mayar da gidan tsohon madugun yan tawayen Biafra na yan kabilar Igbo zalla wajen yawon bude ido.

Odumegu Ojukwu ya jagoranci tawaye na a ware daga hadaddiyar kasar Najeriya sakamakon haka shugaban kasar Najeriya na waccan lokaci Gen. Yakubu Gowon ya ki ya amince bisa wannan dalili yakin basasa ya kaure da ya yi sanadin mumunar zubar da jini tare da jawo asarar rayuka miliyan daya bisa kiyasi.

Ojukwu ya haddasa wannan yakin a 1967 zuwa 1969 wanda daga karshe ya gudu zuwa kasar Ivory coast daga bisani aka ci Igbo da yaki kuma mataimakinsa ya yi saranda ga zaratan Askarawan sojin Najeriya.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN