• Labaran yau


  Kada ku saye man fetur sama da N145 a lita daya - Manajan NNPC Maikanti

  Babban Manajan kamfanin mai na kasa NNPC Maikanti Baru ya bukaci yan Najeriya kada su saye man fetur a farashi da ya wuce N145 kamar yadda Gwamnati ta kayyade.

  Baru ya yi wannan jawabi ne a Abuja jim kadan bayan hukumar da ke sa ido a kan yadda ake tafiyar da harkar sayar da mai da gidajen mai DPR ta rufe wani gidan mai a Abuja mai tambarin NNPC bayan ta kama ana sayar da mai a kan N181 a kowane lita

  Ya kara da cewa NNPC ta tsabtace yadda ake raba man fetur daga matatar mai.Ya kara da cewa yanzu haka an mayar da tsarin bin ka'ida wajen harkar raba mai a Najeriya.


  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kada ku saye man fetur sama da N145 a lita daya - Manajan NNPC Maikanti Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama