Type Here to Get Search Results !

Main event

Yansanda a Lagos sun gano wajen da ake yin Malt da stout na bogi

Rundunar yansanda na jihar Lagos ranar Laraba ta gano wani wajen da ake sarrafa Malt da Stout na bogi a Egbe-Afa a yankin Ikorodu da ke birnin Lagos. An kama mutum biyar da ke da hannu wajen tafiyar da masana'antar na bogi.

Kwamishinan yansanda na jihar Lagos Imohimi Edgal ne ya jagoranci jami'ansa wajen gudanar da aikin yayin da ya nuna ma manema labarai masana'antar da kuma Malt da Stout da ake yi a wajen.

Kawamishina Edgal ya ce rundunarsa za ta gurfanar da wadanda ake zargi a gaban Kotu bayan ta kammala bincike.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies