Yadda mai gidan haya ta yanke masu haya da reza saboda zakaran Easter

Wata mata mai gidan haya ta raunata wasu masu haya a gidanta da reza sakamakon takaddama da ta kai ga musanyar yawu daga bisani ya rikide zuwa dambe tsakaninta da masu haya lamari da ya sa mai gidan haya ta raunata yaro da mahaifiyarsa masu haya.

Rahotanni sun ce yaron dan shekara 12 da mahaifiyarsa yar shekara 38 sun fuskanci hukunci a hannun mai gidan haya mai suna Mrs.Atalekor  a gidanta da ke Ufuoma a Ughelli na jihar Delta bayan zakara da masu haya suka sayo domin bikin Easter ya bata varanda mai gidan haya da kashi.

Sakamakon haka cacan baki ya biyo baya daga bisani dambe ya kaure har da yanka da reza.

Yanzu haka Likitoci na kokarin ceto rayuwar yaron da aka yanka da reza ganin yadda raunin da aka yi masa ya yi muni.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN