• Labaran yau


  Gwamna Bagudu zai ci gaba da taimaka wa manoman jihar Kebbi

  Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya jaddada aniyar gwamnatinsa na taimaka wa manoma a fadin jihar domin a sami wadataccen amfanin gona.

  Gwamnana ya yi wannan jawabin ne a garin Gotomo a karamar hukumar mulki ta Argungu yayin da yake duba fili a fadama da zai dace da noman rake bisa shirin gwamnatinsa na samar da rake zaman makamashi marmakin man fetur.

  Wasu manoma a fadamar ta Gotomo sun zanta da Gwamna akan matsaloli da ke damunsu  yayin da wani manomi ya bukaci Gwamna ya ba su taimako na rancen kudi bisa aniyarsu ta noman rake da Mankani.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Gwamna Bagudu zai ci gaba da taimaka wa manoman jihar Kebbi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama