• Labaran yau


  Yadda za ka yi ma'amala da mara kunya ko maras ragowa a cikin al'umma

  A cikin zamantake na yau da kullum wajibi ne dan adam ya yi mu'amala tare da mutane kala-kala a rayuwarsa, kuma bisa wannan tafiya dole ne ka ka hadu da mutane kala-kala masu hali da suka banbanta da juna.

  Amma idan ka ci karo da mutum mara mutunci ko ragowa yana da kyau ka kula da wadannan ababe:

  1.Idan mara kunya ko mutunci ya ya ci zarafin ka ta hanyar gaya maka kalamai na rashin ragowa, ka gaya masa kai tsaye cewa ya ci zarafin ka .Domin maras ragowa basa kula da cewa sun saba ma wasu hatta sai kai ma ka saba masu.

  2. Ka gaya masa cewa abin da ya fada ba wai shi ne daidai ba domin wasu mutane ma suna da hikima da za su iya bayar da nasu ra'ayi.

  3. Idan ana cikin magana zai dinga yanke maganar wasu yana cusa nashi ba tare da neman afuwa ba, idan haka ya faru kai ma ka yanke nashi ta hanyar nuna masa cewa kuskure ne ya dinga yanke maganar wasu alhali shi ya yi nashi jawabi babu wanda ya katse shi.

  4. Idan ya furta kalamai na rashin ragowa , ka gaya masa cewa wannan kalma ce ta rashin ragowa kuma ka bukaci kada ya kara domin bai fi kowa ba.

  5. Ka kasance mai hakuri da mara kunya da ragowa domin mafi yawa daga cikin su basu san cewa basu da ragowa ba, amma sai ka kaurace masa domin kada ka hada wani lamarin mutunci da shi domin gudun kada ya ci zarafin ka a bainar jama'a nan gaba.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda za ka yi ma'amala da mara kunya ko maras ragowa a cikin al'umma Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama