Naja'atu Muhammad wacce tsohuwar Sanata ce daga jihar Kano ta ce tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya kashe N2bn a kullum wajen harkar tsaro da ya kasa samarwa yan Najeriya. Ta yi wannan jawabi ne a wajen wani taron lakca da BBOG ta shirya a Abuja ranar Asabar,
Ta kuma dora rashin nassara da aka samu wajen tabbatar da tsaro a kan abin da ta kira "rashin sanin ya kamata daga wasu yan siyasa da manyan jami'an soji" wanda ta ci gaba da cewa shi ne ya jawo rashin karewar rikicin boko haram.
Tsohuwar Sanatar wacce ita ce macce ta farko da ta zama Sanata a jihar Kano ta yi zargin cewa "Ali Modu Sheriff ne ya haifar da boko haram lokacin da yake Gwamnan jihar Borno".
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa
isyakulabari@gmail.com
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001.
Shiga cikakken shafinmu.
www.isyaku.com