Type Here to Get Search Results !

Dalilin da ya sa na ce a yi wa shugaba Buhari ruwan duwatsu - Toni Momoh

Wani tsohon Ministan watsa labarai a Najeriya Prince Toni Momoh ya yi bayani a kan dalilin da ya sa ya ce yan Najeriya su jefi Gwamnatin shugaba Buhari da duwatsu matukar ya gaza a shugabanci.

Momoh ya yi wannan jawabi ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben 2015, inda ya bukaci yan Najeriya su jefi gwamnatin APC idan ta kasa.

Ministan ya shaida wa The Sun cewa tuni yan Najeriya suka dade suna jifar shugaba Buhari duk da nassarori da Gwamnatin Buhari ta samu a fannen tsaro musamman ya yankin Borno.

Ya kuma ce a matsayinsa na Minista ya gaya wa jama'a abin da suke son su ji ya kuma rage su da kansu su auna yadda zasu yi da labari da aka ba su.

"Tuni wadansu mutane suna jifar mu, amma wadanda ke wannan jifa yan adawa ne da idonsu ya rufe da  suka gaza ganin nassarori da wannan Gwamnatin ta samu a sassa daban-daban a kasarnan".

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN