Hukumar EFCC reshen jihar Gombe ta gurfanar da tsohon Kakakin Majalisar Dokoki na jihar Taraba Honourable Mark Bako
Useni, Hassan A Abubakar da John Danjuma Ali a gaban babban Kotun tarayya karkajin Justice Filibus
Bitrus Andetur a Jalingo bisa zargin aikata ba daidai ba da dukiyar jama'a.
Hukumar ta yi zargin cewa Mark ya karbi N45m domin amfanin kansa yayin da Arc.Darius Ishaku tsohon dan takarar kujerar Gwamnan jihar taraba tare da John da Hassan suka karbi N267.46m daga badakalar kudi na Diezani saboda a bayar da na goro ga jami'an INEC a jihar Taraba.
Bayan an karanta masu tuhumar da ake yi masu a gaban Kotu, dukan mutanen basu amsa laifin su ba sakamakon haka mai gabatar da kara Abubakar Aliyu ya bukaci Kotu ta sa rana domin a fara shari'ar.
Alkalin Kotun Justice Fibilus ya dage shari'ar zuwa ranar 26l,27 da 28 domin ci gaba da shari'ar ya kuma bayar da belin wadanda ake zargi.
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa
isyakulabari@gmail.com
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001.
Shiga cikakken shafinmu.
www.isyaku.com