Ga dukan
alamu wadansu daga cikin tsofaffin janarorin soji ciki har da wadanda
suka yi shugabancin kasar nan sun juya wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari
baya tare da yunkurin ganin bai sake tsayawa takara a zaben badi ba, ko
kuma idan ya tsaya za su yi duk abin da za su iya wajen ganin bai kai
ga nasara ba.
Janar-Janar din da suka juya wa
Shugaba Buhari bayan sun hada da Cif Olusegun Obasanjo, wanda a watannin
baya ya fitar da wata doguwar wasika yana kira ga Shugaba Buhari cewa
kada ya tsaya takara a zaben na badi
Obasanjo
wanda ya ci gaba da caccakar gwamnatin Buhari a baya-bayan nan a duk
inda ya samu kansa, yana zargin gwamnatin Buhari ne da gazawa a fannin
tattalin arziki da kuma zargin Shugaban kasar da nada ‘danginsa’ a
mukaman gwamnati tare da karkata harkokin tsaro kacokan ga Arewa.
Daga baya ma Obasanjo ya kafa wata
kungiyar siyasa mai da’awar ceto Najeriya, wadda mutane da dama ke
kallon ya kafa ta ce domin hada gangamin kawar da Buhari daga gadon
mulki a zaben na badi.
Yayin da Obasanjo ke ci gaba da
caccakar gwamnatin Buhari ne kwatsam sai Janar Theophilus Yakubu danjuma
ya fito ya ce ’yan Najeriya su fito su kare rayukansu su daina dogaro
da sojojin Najeriya, wadanda ya zarga da hada kai da Fulani makiyaya a
jiharsa ta Taraba suna kashe kabilun yankin.
Janar danjuma ya ma yi gargadin cewa
idan gwamnati ta gaza daukar mataki to abin da yake faruwa a kasar
Somaliya zai zamo wasan yara idan aka kwatanta da abin da zai faru a
Najeriya.
Ana cikin jimamin kalaman Janar
danjuma ne, sai kuma Obasanjo ya sake shigowa fage, inda ya bukaci ’yan
Najeriya cewa kada su yarda su sake zaben gwamnatin da ta gaza a zaben
badi. Obasanjo ya ce “zai zama cikakkiyar wauta a ce ’yan Najeriya sun
sake karfafa gazawa ta hanyar sake zaben gwamnatin da ta kasa yin
katabus kuma gwamnatin da ta gaza a zaben 2019.”
Obasanjo wanda ya bukaci Shugaba
Buhari da Jam’iyyar APC su daina bai wa ’yan Najeriya uzuri ya bayyana
haka ne lokacin da wakilan kungiyar New Nigeria a karkashin jagorancin
Chima Anyaso da Moses Siasia suka ziyarce shi a dakin Karatun Shugaban
kasa da ke Abeokuta a ranar Litinin da ta gabata.
Kamar yadda ya fadi a wasikar da ya
taba rubutawa Obasanjo ya zargi gwamnatin APC da “jawo kunci ga ’yan
Najeriya” da “gudanar da tsarin tattalin arziki marar katabus” wanda ya
ce ya “ruguza harkokin kasuwanci.”
Ya bayyana gwamnatin APC da “wadda
ta gaza” kuma ya gargadi ’yan Najeriya cewa kada su sake zaben
“kasasshiyar gwamnati da kullum ke neman uzuri kan gazawarta wajen cimma
bukatun ’yan Najeriya.”
Sai dai kuma matsayin nasa bai bar
Jam’iyyar PDP ba, inda ya ce kada ’yan Najeriya su rudu da neman gafara
da PDP ta yi, inda ya ce PDP da APC, ba za su iya fitar da Najeriya daga
tabarbarewar tattalin arziki ba.
Shi ma tsohon Shugaban kasa Janar
Ibrahim Babangida ya bi sahun su Obasanjo, inda ya ce lokaci ya yi da
tsofaffi za su mika harkokin mulki ga matasa su jagoranci kasar nan,
inda ya ce, tsofaffin sun dade a harkokin mulki kuma tunaninsu irin na
da ne.
Babangida ya bayyana haka ne lokacin
da shugabannin kungiyar New Nigeria a karkashin Moses Siloko Siasia
suka zaiyarce a gidansa da ke Minna.
Sai dai Janar Babangida ya nuna
halinsa na Maradona, inda ya ki fitowa ya ambaci Shugaba Buhari
kai-tsaye, amma ya ce: “Tarihi ya nuna cewa ci gaban kowace kasa ya fi
gudana a hannun matasa da suke cike da sababbin dabaru. Wadansu daga
cikinmu sun zama shugabanni suna da karancin shekaru. Tsofaffi nan ya
kamata su ba da hanya ga matasa. Yanzu mun zama tsofaffin yayi yanzu
lokaci ne na masu jini a jika, don haka a karfafa wa matasa su yi amfani
da iliminsu na zamani don kai kasar nan gaba.”
Wata jaridar da ake bugawa a Intanet
mai suna AljazirahNigeria ta ruwaito a ranar 2 ga Afrilun nan cewa,
Janar T.Y. danjuma ya fara tuntubar Janar Obasanjo da Janar Babangida da
Janar Abdulsalami Abubakar da sauransu domin ganin Buhari bai kai
labari ba a zaben na badi. Jaridar ta ce, a watan jiya ne Janar T. Y.
danjuma ya fara wannan yunkuri lokacin da ya ziyarci tsohon Mataimakin
Shugaban kasa Atiku Abubakar, ya bukaci su ajiye dukan sabanin da ke
tsakaninsu don ceto kasar nan daga abin da ya kira kokarin rugujewa.
Wata majiya mai tushe kuma ta kusa
da tsohon Mataimakin Shugaban kasar ta shaida wa AljazirahNigeria cewa:
“T.Y. danjuma ne ya tsara ganawar. Kuma ya shaida wa Atiku cewa wajibi
ne su yi aiki tare domin tabbatar da Shugaba Buhari da mutanensa ba su
dawo kan gadon mulki ba.”
Majiyar ta ruwaito Janar din yana
cewa: “Wadannan mutane suna son ruguza kasar nan. Wajibi ne mu jingine
dukan bambance-bambancenmu a gefe mu tabbatar ba su dawo gadon mulki a
shekarar 2019 ba. kasar nan ta fada cikin rikici. Fulani makiyaya sun
haukace, amma ba su cewa komai, kuma ba su yin komai. Idan kasar ta
dare, ni da kai ne za mu fi shan wahala. Wadancan mutane ba su da abin
da za su rasa. Ba su da wani kamfani a nan. Idan rikici ya balle, za su
kwashe iyalansu ne kawai su gudu. Babu abin da za su yi asara. Mu ne
manyan wadanda za su yi asara.”
Jaridar ta kara da cewa: “Tsohon
Ministan Tsaron ya ce: “Yadda Fulani makiyaya suke dada baje kolinsu
idan muka kyale su, kasar nan za ta kama da wuta. Don haka wajibi ne mu
yi duk abin da ya wajaba don dinke kasar nan, hadin kan da sai mun yi
aiki sosai kafin a cim masa da tabbatar da dorewarsa.”
Majiyar ta shaida wa jaridar cewa:
“Janar (TY danjuma) daga nan ya je wurin IBB (tsohon Shugaban Soji
Ibrahim Badamasi Babangida) da Abdulsalami (tsohon Shugaban Mulkin Soji
Abdulsalami Abubakar) kan su taimaka wajen hado kan janarori domin su
shawo kan Cif Olusegun Obasanjo ya mayar da wukarsa kube ta yadda
dukansu za su tattaro jama’a su samar da dukiyar da za su mara wa Atiku
Abubakar baya.”
Majiyar ta kara da cewa: “Janar
danjuma ya kuma roki Atiku cewa zangon mulki daya kawai zai yi don mulki
ya koma Kudu ta yadda mutanen Kudu ba za su ji a tauye su ba. Kuma ya
ce wajibi ne su hada karfi da karfe wajen hade kan dukan shiyyoyin
siyasa da kabilun kasar nan. ‘Ko a Arewa ba mu taba ganin irin wannan
rarrabuwa ba,’ inji Janar danjuma.
Sai dai a ranar Talatar da ta
gabata, Kakakin Shugaba Buhari, Femi Adesina ya ce gwamnati ba za ta ce
komai kan kalaman Cif Obasanjo game da gwamnatin Buhari ba.
A yayin da yake amsa tamayoyi a
gidan talabijin na Channels, Femi Adesina ya ce, “Martanin da Ministan
Labarai, Lai Mohammed, ya mayar wa Obasanjo a watannin baya, sun magance
dukan zarge-zargen nasa na baya-bayan nan baki daya.”
Adesina ya kara da cewa gwamnatin
Buhari ta samu nasarar magance matsalolin kasar da suka shafi tattalin
arzikin da tsaro, inda Najeriya ta samar da rara a asusunta na waje
wadda ba a taba samun irinta ba a tarihin kasar. Don haka ya ce wannan
suka ta Obasanjo ba za ta hana Gwamnatin APC ci gaba da bayyana wa ’yan
Najeriya irin barnar da gwamnatin da ta shude ta tafka ba.
Sai dai a yayin da gwamnatin ta
kauce wa mayar wa Obasanjo martani wani jigo a kungiyar Yarbawa ta
Afenifere, Cif Ayo Adebanjo ya nuna kaduwa da caccakar da Obasanjo ya yi
ga Shugaba Buhari a baya-bayan nan, inda ya ce, Obasanjo ba ya da
mutuncin da zai iya zargin wani da gazawa.
Adebanjo wanda yake magana a wajen
gabatar da littafin rayuwarsa mai suna “Tell it as it is- Fadi abin
yadda yake,” a Legas a ranar Talatar da ta gabata ya bayyana tsohon
Shugaban kasar da ‘Tauraruwa mai wutsiya.’
Cif Adebanjo ya ce, idan da Najeriya
tana cike da mutane masu mutunci, mutane irin su Obasanjo ba za su sake
iya shiga mutane ba, inda ya ce yana jin mamakin yadda mutane suke ci
gaba da ba tsohon Shugaban kasa “martabar da ba ta kamata ba, lura da
sanin halayensa.”
Ya ce yana da tabbacin cewa “Lokacin
da gwamnatin talakawa ta gaskiya ta hau mulki, za ta kwace dakin Karatu
na Shugaba Obasanjo da ke Abeokuta” daga tsohon Shugaban kasar.
Adebanjo wanda zai cika shekara 90 a duniya a ranar 10 ga Afrilun nan,
ya yi kaca-kaca da tsohon Shugaba kasa Obasanjo musamman a babi na 13
shafi na 233 mai taken: ‘Awolowo, Obasanjo da kasar Yarbawa.’
Cif Ayo Adebanjo ya bayyana mulkin Cif Obasanjo da cewa shi ne mulki mafi zama annoba ga kasar nan.
Daga Aminiya
Tags:
LABARI