Tsohon mai ba shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara a fannin tsaro Col. Sambo Dasuki Rtd. ya maka Lawal Daura da SSS, tare da Atoni janar na Najeriya Abubakar Malami a gaban wata babbar Kotun tarayya a Abuja inda yake neman a biya shi N5b sakamakon tsare shi da hukumar take ci gaba da yi tun 2015.
Hukumar SSS ta kama Sambo Dasuki bisa zargin mallakar makami ba bisa ka'ida ba tare da wasu karin tuhuma na almundahana da kudi ba bisa ka'ida ba wanda hukumar EFCC ta gurfanar da shi a gaban Kotu.
Karar wanda aka mika wa Alkali Ahmed Muhammed na wata babban Kotu ba a sa ranar da za a saurara ba.
A watan da ya gabata Kotun koli na Najeriya ta bayar da umarni cewa babbar Kotu da ke Maitama Abuja ta gaggauta sauraron shari'ar da ake yi ma Sambo Dasuki.
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa
isyakulabari@gmail.com
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001.
Shiga cikakken shafinmu.
www.isyaku.com