B-kebbi: Lalata da karamar yarinya a Badariya, Kotu ta hana belin wanda ake zargi

Babban Kotun Majistare mai daraja ta 1 da ke garin Birnin kebbi ta ki ta bayar da belin wani dan kabilar Igbo wanda ake zargi da yin lalata da wata yarinya Bahausa yar shekara 12 a unguwar Badariya ranar 19 ga watan Maris 2018.

Alkalin Kotun Justice Kakale Mungadi ya ce Kotu ta yi la'akari da yanayin tuhuma da kuma tafiyar shari'ar ganin yadda aka aikata laifin da ake zato ya haifar da gibin tsaro ga wanda aka yi kara.Sakamakon haka Kotu ta ki ta bayar da belinsa bisa dalilin tsaron lafiyar sa.

Bayan Justice Kakale Mungadi ya saurari Lauyan wanda ake zargi Barr.B.A Isaak tare da shaidan mai gabatar da kara Insp. Isah, Alkalin Kotu ya dage shari'ar har zuwa ranar 14 ga watan Aprilu domin ci gaba da shari'ar yayin da ya bayar da umurni a tasa keyar wanda ake tuhuma zuwa Kurkuku.

Daga Isyaku Garba a Birnin kebbi.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN