Type Here to Get Search Results !

Yadda garkame Salman Khan a Kurkuku ya bakanta ran yan Bollywood

Samun fitaccen jarumin finafinan Bolly Salman Khan da laifi da wata Kotun Jodhpur ta yi ranar Alhamis ya bakanta wa wasu jigajigai a masana'antar finafinai na Bollywood rai kamar  Jaya Bachchan, Subhash Ghai da Alok Nath wadanda manyan masu shirya finafinai ne a masana'antar.Amma mutanen sun ce suna kyautata zaton cewa Salman zai sami adalci a Kotu na gaba.

Kotu ta sami Salman Khan da laifin kashe gada ranar 1-2 ga watan Oktoba yayin da ake gudanar da wani fim Hum Saath Saath Hain a 1989 a kauyen Kankani wanda ya saba wa dokokin kiyaye halittun gandun daji na jihar Jodhpur karkashin sashe na 9/51 dokokin kiyaye haluttun daji 1972.

Yayin da Kotu ta daure Salman Khan a Kurkuku, Kotun ta sallami wasu jarumain finafinan Bollywood guda hudu da aka hada tare da su a cikin tuhumar watau Sonali Bendre, Saif Ali Khan, Tabu da Neelam.

Tuni Lauyan Khan ya shigar da bukatar daukaka kara ga Kotu na gaba tare da bukatar bayar da shi beli. Yanzu haka Khan na Kurkukun Jodhpur mai lamba 106.

Sai dai ranar Asabar Kotun daukaka kara ta bayar da belin Salman Khan a kan Rupee 50.000 tare da sallamarsa a bisa matsayin beli.Bayan fitowarsa daga Kurkuku, Salman ya zarce kai tsaye zuwa filin jirgin sama inda ya tashi zuwa Mumbai garin sa na haihuwa.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN