• Labaran yau


  Tecno ta ce Najeriya ce ke samar da babbar kasuwa a Afrika

  Kampanin wayar salula Tecno ta ce Najeriya ce ke samar mata da babbar kasuwa mafi girma a Nahiyar Afrika duk da kalubale da ake samu a wasu gurbi na kasuwar.

  Wani jigo a kampanin Tecno a Najeriya Mr. Andy Yan ya shaida haka a wani taro na kaddamar da Tecno Global Sprint  ranar Alhamis a Eko Hotel and Suites da ke garin Lagos.

  Mr Yan ya ce Tecno ta samar wa matasa aiki a Najeriya tare da basu horo a gurbi da dama kan harkar wayar salula.

  Ya yi kira ga Mahukuntar Najeriya domin su samar da ingantacce kuma dauwamammen tsari na kariya ga yanayin kasuwanci domin samar da tsaro da zai sa kamfuna su zuba jari hankali kwance a kan harkar wayar salula musamman Tecno a Najeriya.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Tecno ta ce Najeriya ce ke samar da babbar kasuwa a Afrika Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama